Babu batun sayar da Aston Villa

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Villa na kokarin taka rawar gani a Premier

Kocin Aston Villa, Tim Sherwoord, ya ce babu maganar sayar da kulob din a halin yanzu.

Shugaban Aston Villa Randy Lerner ne ya fara tattauna wa kan sayar da Villa £150m, amma har zuwa lokacin da aka tsaida sayar da kulob din ba a cimma matsaya ba.

A watan Mayu wasu rukunan masu hannun jari karkashin tsohon daraktan Chelsea, Paul Smith, suka taya Villa.

Kuma a watan na Mayu Lerner wanda ya sayi kulob din £62.6m a shekarar 2006 ya saka shi a kasuwa.

Sherwoord ya kuma ce yana fatan Christian Benteke da kuma Fabian Delph za su ci gaba da murza leda a Villa Park.