Za a gabatar da Oliseh a matsayin kociyan Eagles

Image caption Oliseh zai jagoranci Super Eagles ne a lokacin da kungiyar ke fuskantar kalubale da dama.

Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya, NFF za ta gabatar da Sunday Ogorchukwu Oliseh ga manema labarai da al'ummar kasar a matsayin sabon kociyan Super Eagles.

Shugaban NFF Amaju Pinnick, da sauran manyan jami'an hukumar za su gabatar da Oliseh ga bainar jama'a ne a ranar Laraba a babban filin wasa na kasar da karfe 11 na safe.

A ranar Tatala da almuru, Oliseh da mataimakansa sun gana da kwamitin gudanarwa na hukumar ta wanda Chief Felix Anyansi-Agwu ke jagoranta, domin su bayyana irin tsare-tsaren da za su yi wajen inganta kungiyar ta Super Eagles.

Oliseh, wanda ake yi wa lakabi da 'Passmaster' lokacin da yake kan ganiyarsa ta taka leda, ya samu lambar zinare a gasar kwallon kafar Olympic; ya ci kyautar zinare da azurfa da tagulla a gasar cin kofin nahiyar Afrika, sannan yana cikin 'yan wasan da suka bugawa Super Eagles wasan da ta kai matakin karshe na gasar cin kofin kwallon kafar duniya a shekarar 1998.

Babban kalubalen da ke gaban Oliseh shi ne yadda zai shirya Super Eagles domin tunkarar wasannin cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekarar 2017, wadda za a yi a Tanzania a farkon watan Satumba da kuma wasannin sada zumunta da za su biyo baya.