'Ina kwallo tukuru da ya sa ni yin fice'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gyan ya koma China

Kyaftin din Ghana Asamoah Gyan ya karyata cewar ya koma Shanghai SIPG domin yawan kudin da zai dinga karba.

Gyan mai shekaru 29, ya ce ya koma China da murza leda domin ya nuna kwarewarsa a fagen tamaula a kasar.

Dan wasan ya buga wa kungiyar Al Ain ta Hadaddiyar Daulal Larabawa kwallo tsawon shekaru hudu.

Gyan ya shaida wa BBC cewar “Ban san dalilin yin sukar ba, ina yin aiki tukuru da hakan ya sa na yi fice, ina kuma mai da hankali kan aikin dana sa a gaba na”.

Dan wasan ya maida martini ne kan zargin da wasu suke yi cewar ya ki zuwa ya buga babbar gasa da fitattun kungiyoyi domin ya samu arziki.

Gyan ya ce ana murza kwallo mai kayatar wa a China, kuma shi kansa har yanzu yana zura kwallaye a raga.