Real Madrid ce kan gaba a daraja a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon kocin Real Madrid, Rafael Benitez

Real Madrid ne kulob din wasa da ya fi daraja a duniya in ji mujallar Forbes.

Wannan ne karo na uku da Madrid ke rike da wanan matsayin a rahoton da Forbes kan fitar duk shekara.

Mujallar ta ce Madrid tana da kadarar £2.08bn, kungiyar kwallon zari rigur amurka Dallas Cow Boy ve ta biyu sai New York Yankees ta uku.

Barcelona tana mataki na hudu da kadarar £2.02bn, Manchester United mai kadarar £1.98bn ta yi kasa zuwa mataki na biyar daga matsayi na uku da take kai a bara.

Sauran kungiyoyin da suke goman farko sun hada da Los Angeles Lakers da New York Knicks da New England Patriots da Washington Redskins da kuma Los Angeles Dodgers.

Manchester City mai kadarar £890m tana mataki na 29, sai Chelsea ta 31 da kadarar £877m, yayin da Arsenal ke mataki na 36 da kadarar £839m.