Robinho ya koma Guangzhou Evergrande

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Robinho ya murza leda a Manchester City

Tsohon dan kwallon Real Madrid da Manchester City Robinho ya koma taka leda Guangzhou Evergrande a China.

Robinho dan kwallo Brazil ya saka hannu kan yarjejeniyar watanni shida.

Dan wasan mai shekaru 31, zai taka leda da abokin wasansa a Brazil Paulinho kuma karkashin Luiz Felipe Scolari.

Robinho wanda ya yi wa AC Milan wasa zai saka riga mai lamba 60 a China.