Vidal na gab da koma wa Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Vidal ya haskaka a Juventus

Dan kwallon Juventus Arturo Vidal na gab da koma wa Bayern Munich amma ba a kamalla kulla yarjejeniyar ba.

"Muna zawarcinsa amma ba a kamalla komai ba," in ji shugaban Bayern Karl-Heinz Rummenigge.

Kungiyoyin biyu sun shafe sa'o'i 24 suna tattaunawa kan dan kwallon Chile din mai shekaru 29.

Tun lokacin da Vidal yake Bayer Leverkusen take son ta saye shi.

Kungiyoyin gasar Premier kamar su Manchester United da Arsenal suma suna zawarcin Vidal.