Za a zabi shugaban FIFA a watan Fabrairu

Hakkin mallakar hoto FIFA.com
Image caption Blatter ya fusata bayan an jefe shi.

Jami'an hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, sun ce za a zabi sabon shugabanta ranar 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2016 a birnin Zurich.

A watan jiya ne shugaban hukumar, Sepp Blatter, ya bayyana cewa zai sauka daga mukamin bayan an kama manyan jami'an hukumar bisa zargin cin hanci da rashawa.

A ranar Litinin ne manyan jami'an hukumar ke yin taro a Zurich, inda suke tattaunawa kan sauye-sauyen da za a yi wa hukumar -- ciki har da iyakance wa'adin shekaru 12 ga duk mutanen da za su shugabanci hukumar da kuma wallafa albashin da ake bai wa shugabanninta domin kowa ya sani.

Blatter ya yi fushi

Ana tsakiyar taron ne, a lokacin da Blatter ke yi wa manema labarai jawabi, sai wani mutum ya tsaya a gabansa, kana ya rika magana da 'yan jarida, kuma daga bisani ya jefe shi da takardun da ke hannayensa.

Lamarin dai ya fusata Mr Blatter har ta kai ga ya fice daga zauren, yana mai cewa ba zai dawo ba sai komai ya daidaita.