Za a ci gaba da Federation Cup

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Tuni aka fitar da Enyimba da Kano Pillars daga wasannin

Ranar Laraba za a ci gaba da buga gasar Federation Cup ta Nigeria wasannin kungiyoyi 16 da suka rage.

Cikin wasannin da za a fafata, Remo Stars za ta buga da Lobi Stars da na Nasarawa United da Abia Warriors da kuma kai ruwa rana tsakanin Plateau United da El-Kanemi Warrioris.

Prime FC za ta yi gumurzu da Akwa United da kuma karin batta tsakanin Ifenyiubah da FC Taraba.

Karawa tsakanin Kwara United da Enugu Rangers sai a ranar Alhamis za su raba raini.

Ga ainihin jadawalin wasannin da za a buga a Confederation Cup din:

Laraba, 22 July, 2015

  • Remo Stars v Lobi Stars
  • Heartland v BJ Foundation
  • Plateau Utd v El-Kanemi Warriors
  • Nasarawa Utd v Abia Warriors
  • FC Ifeanyiubah v FC Taraba
  • Prime FC v Akwa Utd
  • Tornadoes Feeders v Dolphins

Alhamis, 23 July, 2015

  • Kwara Utd v Rangers