Newcastle Unitred ta dauki Aleksandar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mitrovich shi ne kan gaba wajen zura kwallaye a gasar Belgium a inda ya ci 20 a bara.

Kungiyar Newcastle United ta kulla yarjejeniyar da dan wasan Anderlecht Aleksander Mitrovic kan kudi £13m domin ya buga mata tamaula.

Mitrovich dan kwallon Serbia, mai shekaru 20, ya saka hannu kan kwantiragin shekaru biyar.

Dan wasan ya zura kwallaye 36 a raga a shekaru biyu da ya taka leda a Belgium, ciki har da guda 20 da ya ci a bara.

Anderlecht ta sayo Mitrovich daga Partizan Belgrade kan kudi £4.3m a shekaru biyu da suka wuce.

Newcastle ta dauko 'yan kwallo biyu a bana kenan, bayan da ta fara sayo Georginio Wijnaldum daga PSG.