Rooney zai koma mai cin kwallo a United

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Van Gaal na fatan ganin United ta taka rawar gani a kakar wasannin bana

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce yana shirin ya yi amfani da Wayne Rooney a matsayin mai cin kwallo a kulob din.

Rooney mai shekaru 29, yana buga wa United wasanni daga tsakiya tun a kakar wasannin bara.

Van Gaal ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake ganawa da 'yan jaridu kan wasan da za su buga da San Jose Earthquakes ranar Laraba.

Rabon da Rooney ya buga matsayin mai ci wa United kwallo tun a kakar wasan 2011-12, a inda ya zura kwallaye 34 a raga.

Tuni ma dan wasan ya ce yana fatan ya ci kwallaye 20 ko fiye da haka idan ya fara buga wa United a sabon matsayin da za a ba shi.