Barcelona ta doke LA Galaxy a Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suarez da Gerrard tsoffin 'yan wasan kungiyar Liverpool ne.

'Yan kallo 93,226 suka kalli karawar da Barcelona ta doke LA Galaxy 2-1 a wasan atisayen tunkarar wasannin bana a California.

Wannan shi ne karon farko da filin wasa na Pasadena Rose Bowl ya karbi yawan 'yan kallo a fafatawar da ya hada da kulob din Amurka mai buga Major League Soccer.

Galaxy ta saka Steven Gerrard a wasan da ya fuskanci tsohon abokin da suka buga tamaula wato Luis Suarez har ma suka yi musayar riga bayan da aka sauya su.

Yawancin wadan da suka kalli karawar sun saka riga mai ruwan shudi dauke kuma da kalle mai tambarin Barcelona.

Barcelona za ta kara da Manchester United a Santa Clara ranar Asaabar, sannan ta yi gumurzu da Chelsea a Washington ranar 28 ga watan Yuli.