Liverpool ta kammala daukar Benteke

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Benteke bai buga wa Belgium gasar cin kofin duniya a Brazil ba, bisa raunin da ya yi jinya

Liverpool ta kammala sayen Christian Benteke daga Aston Villa kan kudi £32.5m.

Benteke mai shekaru 24, ya amince da kulla yarjejeniya mai tsawo da zai taka leda a Anfield, kuma shi ne dan kwallo na biyu da Liverpool ta saya ma fi tsada a bana.

Dan wasan Belgium ya ci kwallaye 49 daga wasanni 101 daya buga wa Villa tun komawarsa kulob din daga Genk kan kudi £7m a shekarar 2012.

Benteke shi ne dan wasa na bakwai da Liverpool ta sayo a bana, bayan da ta sayar da Raheem Sterling ga Manchester City kan kudi £49m.