Depay ya ci wa Man United kwallo a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana fatan ta taka rawar gani a kakar wasan bana

Memphis Depay ya ci wa Manchester United kwallo a wasan da ta doke San Jose Earthquakes 3-1 a Amurka ranar Laraba.

Depay dan kwallon Netherlands ya yi amfani da damar da ya samu ya kuma ci kwallo ta biyu saura minti takwas a ta fi hutun rabin lokaci.

Juan mata ne ya fara ci wa United kwallo, kafin Fatai Alashe ya zare kwallon da aka ci su, kuma Andreas Pereira ne ya kara ta uku a wasan.

Tsohon kocin United Sir Alex Ferguson ya kalli fafatawar da kulob din ya samu nasara a shirin da ya ke yi na tunkarar wasannin bana.

United ta lashe wasanni biyu kenan da ta yi za kuma ta fafata da Barcelona a Santa Clara ranar Asabar.