West Ham ta dauki Manuel Lanzini

Hakkin mallakar hoto westhamunited
Image caption West Ham United ta dauko 'yan wasa bakwai kenan jumulla a bana

Manuel Lanzini ya koma West Ham da taka leda aro daga kungiyar Al Jazira ta Hadaddiyar Daulal Larabawa.

West Ham tana da damar daukar Lanzini mai shekaru 22, idan ya taka rawar gani a kungiyar.

Lanzini tsohon dan wasan River Plate da Fluminense zai buga tamaula aro har zuwa karshen kakar wasannin da za a fara a bana.

Dan kwallon ya yi wa Agentina wasanni hudu a tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 20.

West Ham ta dauko 'yan wasa bakwai kenan a bana da suka hada da Dimitri Payet da Angelo Ogbonna da Pedro Obiang da Carl Jenkinson da Stephen Hendrie da kuma Darren Randolph.