Mourinho ya goyi bayan Asmir Begovic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Begovic ya koma Chelsea kan fam £8m daga Stoke City a watan jiya

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya kare sabon golan da ya sayo Asmir Begovic bisa kwallaye hudun da aka ci shi a wasan farko da ya yi a Amurka.

Chelsea ta sha kashi a hannun New York Red Bulls da ci 4-2 a wasan sada zumunta domin tunkarar wasannin bana.

Begovic mai shekaru 28, ya shiga karawar ne bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, amma aka zura masa kwallaye hudu a raga.

Mourinho ya ce da a ce sun lashe wasan da ci 10-0 ba zai yi farin ciki ba, domin hakan na nufin sun samu wasan tubus-tubus kenan.

Kocin ya ce mai tsaron ragar ba shi da kuzari sosai bisa gajiyar da ya yi a wajen atisaye, amma zai fara saka shi a wasan da za su yi da PSG.

Chelsea za ta fafata da Paris St-Germain a Arewacin Carolina ranar Asabar, sannan ta yi gumurzu da Barcelona a Washington DC ranar 29 ga watan Yuli.