Ozil zai yi wasa mafi kayatarwa a bana - Wenger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wenger ya ce lokaci ya yi da Ozil zai nuna kwarewarsa a murza tamaula

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce Mesut Ozil zai murza leda mafi kayatarwa tun komawarsa kulob din.

Ozil dan kwallon Jamus bai kai kan ganiyarsa a wasanninsa ba, tun lokacin da ya koma Emirates daga Real Madrid kan kudi £42.6m a Satumbar 2013.

Dan kwallon bai buga wa Arsenal wasanni da dama a farkon kakar bara ba, sai da aka juya wasannin zagaye na biyu ya dawo da tagomashinsa.

Ozil ya ci kwallo a wasan sada zumunta da Arsenal ta doke Lyon da ci 6-0, kuma Wenger ya na fatan dan kwallon zai taka rawar gani a kakar wasannin bana.

Daraktan Arsenal Lord Harris ya fada a farkon makwonnan cewar suna goyon bayan Wenger idan zai dauko dan wasa mai zura kwallo a raga komai tsadarsa.