An raba jadawalin Afirka a shiga kofin duniya

Hakkin mallakar hoto kirill kudryavtsev getty
Image caption Samuel Eto'o yana daga cikin wadanda suka taimaka da aka raba jaddawalin wasannin

A ranar Asabar aka fitar da jadawalin wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya a St Petersburg da nahiyar Afirka za ta halatta a 2018 da za a yi a Rasha.

Kasashen Afirka 53 aka raba su zuwa rukunnai, in ban da Zimbabwe wacce Fifa ta kora bisa kasa biyan kudin kociyanta.

An ware wa Nahiyar Afirka gurbin kasashe biyar da za su wakilceta a Rasha a wasannin da za a fara daga 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli.

Za'a buga wasanni har zagaye uku kafin a fitar da kasashe biyar da za su wakilci Afirka a gasar kofin duniyar.

Zagayen farko zai kunshi kasashe 26 da suke baya a jerin da Fifa ta fitar wadanda suka fi iya taka leda a Afirka.

Wadanda suka yi nasara za su hadu da sauran kasashe 27 da suka fi yin fice a jerin kasashen da suka fi iya murza leda a Afirka.

Zagayen karshe kuwa zai kunshi rukunin biyar dauke da kasashe hudu kowanne, da za su kara gida da waje, daga karshe duk wanda ya yi na daya a rukunin shi ne zai wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya a 2018.