Walcott na daf da sabunta zamansa a Emirates

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A 2013 Walcott ya sabunta kwantiragin shekaru uku da rabi a Emirates kan kudi £100,000 a duk mako

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce Theo Walcott ya kusa saka hannu a sabuwar yarjejeniya a Emirates.

Walcott mai shekaru 26, dan kwallon Ingila, saura shekara daya kwantiraginsa ya kare da Arsenal.

Dan wasan ya koma Arsenal daga Southampton a 2006 yana da shekaru 16 da haihuwa, tun daga lokacin ya buga wasanni 302, yayin da ya ci kwallaye 76.

Da aka tambayi Wenger ko Walcott ya sabunta kwantiraginsa da Arsenal ? Sai kociyan ya ce muna fatan nan ba da dadewa ba zai saka hannu kan ci gaba da zama a Arsenal.

Haka kuma mai tsaron ragar Arsenal Wojciech Szczesny na daf da komawa Roma da taka leda, a inda likitocin kulob din za su duba lafiyarsa ranar Litinin.