Aston Villa ta sayo Jordan Ayew

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jordan Ayew ya wakilci Ghana a wasannin cin kofin Afirka a Equatorial Guinea

Aston Villa ta dauko dan kwallon tawagar Ghana Jordan Ayew daga kulob din Lorient na Faransa.

Ayew mai shekaru 23, ya taimakawa Ghana lashe azurfa a gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2015.

Villa ta sayo Ayew ne bayan da ta sayar da dan wasanta mai zura kwallo a raga Christian Benteke ga Liverpool kan kudi £32.5m.

Haka kuma Villa wacce ta sayar da Fabian Delph ga Manchester City, ta dauko Jordan Amavi da Idrissa Gueye da Scott Sinclair da Micah Richards da kuma Mark Bunn.