Drogba ya koma Amurka da murza leda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tauraruwar Drogba ta haska ne tun lokacin da ya koma Chelsea da taka leda

Tsohon dan kwallon Chelsea Didier Drogba ya saka hannu a kulob din Montreal wacce ke buga gasar Amurka wato Major League Soccer.

Drogba mai shekaru 37 ya bar Stamford Bridge a bara, bayan da ya yi wasanni 381, sannan ya lashe kofunan Premier hudu a karo biyu da ya yi wasa a Chelsea.

Shugaban Montreal, Joey Saputo, ya ce dauko Drogba da suka yi itace babbar rana a tarihin kungiyar.

Drogba shi ne dan kwallon tawagar Ivory Coast da ya fi yawan cin kwallaye, yayin da ya zura 65 a raga daga wasanni 105 da ya yi.

Drogba ya bi sawun abokin wasansa a Chelsea Frank Lampard, wanda ya koma murza leda Amurka a kulob din New York City.