Wenger ya yi watsi da kalaman Mourinho

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Petr Cech Arsenal ta sayo daga Chelsea a bana

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce daukar 'yan wasa da wasu kungiyoyi ke yi, ba zai rinjaye shi sauya salon yadda yake sayo yan kwallo ba.

Arsenal wacce ta dauki FA, tana shirin fafatawa da Chelsea wacce ta lashe kofin Premier a wasan Community Shield ranar lahadi a Wembley.

A ranar Litinin Jose Mourinho ya ce sayayyar 'yan kwallo da Arsenal ta yi a shekarun baya, ya dara wanda Chelsea take yi.

Sai dai kuma Wenger ya mayar da martani da cewar "Ba ya sayo 'yan wasa sai yana da bukatar hakan, kuma baya sauraron abin da wasu za su yi tunani ko kuma za su ce".

A watan Mayu Arsenal ta dauki kofin FA karo na biyu a jere, kuma ta kammala a mataki na uku a kan teburin Premier.

Mai tsaron ragar Chelsea Petr Cech ne kawai Arsenal ta sayo, duk da ikirarin da Daraktan kulob din Lord Harris ya yi cewar za su iya dauko kowanne irin dan kwallo zuwa Emirates.

Mourinho ya ce Arsenal tana daga cikin kungiyoyin da za'a yi ribibin lashe kofin Premier bana, ganin yawan 'yan wasan da ta dauko a shekarun baya.