'Berahino bai shirya komawa Tottenham ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham tana zawarcin Saido Berahino ya buga mata tamaula

Dan wasan West Brom, Saido Berahino, bai shirya komawa taka leda Tottenham ba in ji tsohon kociyansa Alan Irvine.

Berahino mai shekaru 21, dan wasan Ingila, ya ci kwallaye 14 a gasar Premier a bara, kuma ana rade-radin zai koma murza leda Tottenham.

Irvine ya ce Berahino bai shirya yin wasa a Tottenham wacce take hankoron samun matsayi na hudu a gasar Premier ba.

Irvine ya horas da West Brom a farkon kakar bara a inda Berahino ya yi wasanni 22 a karkashinsa sannan ya ci kwallaye takwas.

Kocin ya ce ya kamata Berahino ya ci gaba da buga tamaula tukuru da zai ba shi damar yin fice kafin ya koma wata kungiyar da taka leda.