Szczesny ya koma taka leda Roma

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wojciech Szczesny ya koma Arsenal wasa a 2006

Mai tsaron ragar Arsenal, Wojciech Szczesny, ya koma Roma ta Italiya, domin ya taka leda aro, har zuwa karshen kakar wasan bana.

David Ospina ne ya maye gurbin Szczesny mai shekaru 25, a kakar bara, kuma Arsenal ta sayo mai tsaron ragar Chelsea Petr Cech a watan jiya.

Szczesny dan kwallon Poland ya buga wasanni 180 a Arsenal, tun lokacin da ya koma Emirates daga Legia Warsaw a 2006.

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce Szczesny ya samu kwarewa a Arsenal tun yana da shekaru 20, saboda haka za su more shi idan ya kammala zama a Roma.