Mourinho ya zargi Benitez da lalata Inter Milan

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mourinho ya sake komawa horas da Chelsea a karo na biyu

Jose Mourinho ya zargi kociyan Real Madrid Rafeal Benitez da lalata Inter Milan wacce ta fi yin fice a Turai, bayan da ya karbi aikin horas da kungiyar a 2010.

Mourinho ya yi wannan kalamin ne bisa batun da matar Benitez ta yi cewar mijinta zai gyara barnar da Mourinho ya yi a Real.

Benitez wanda yake jagorantar Real Madrid ya kuma horas da Chelsea, ko da yake bai maye gurbin Mourinho kai tsaye ba a Stamford Bridge.

Mourinho ya ce Benitez ya je Chelsea ne a inda ya maye gurbin Roberto Di Matteo, yayin da ya koma Real Madrid ya maye gurbin Carlo Ancelotti.

Kociyan ya kara da cewa Benitez ya maye gurbinsa a Inter Milan, kuma a watanni shida ya hargitsa kungiyar da ta fi yin fice a Turai a lokacin da ya Horas da ita.

Mourinho ya ce ya kamata Montserrat Seara, ta mai da hankali kan kula da mijinta, ba wai ta dunga maganganu a kansa ba.