Mexico ta kori kociyanta bisa dukan dan jarida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Herrera shi ne ya jagoranci Mexico lashe Gold Cup

Hukumar kwallon kafar Mexico ta sallami kociyanta Miguel Herrera, kwanaki biyu da ya lashe Gold Cup, bisa zargin ya naushi dan jarida.

Dan jaridar wanda yake aiki da wani gidan talabijin ya ce kociyan ya doke shi a wuya sannan kuma ya yi masa barazana a filin jirgin sama a Philadelphia.

Shugaban hukumar kwallon kafar Mexico mai jiran gado Decio de Maria ya ce laifin da mai horaswar ya aikata ya sada da mutunta da kuma daraja wasanni.

Ya kuma fara aiki da tawagar kwallon kafar Mexico a Oktoban 2013, kuma shi ne kociya na hudu da kasar ta dauko a cikin watanni shida a lokacin.