Platini zai yi takarar shugabancin FIFA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Fifa Sepp blatter da shugaban EUFA Platini

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini, ya bayyana kudurinsa na son tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Platini ya ce yana son dawo wa da hukumar FIFA martabarta ne da ta kamace ta.

Shugaban FIFA mai ci yanzu Sepp Blatter, ya sanar da aniyarsa ta barin mukamin nasa a watan da ya gabata, kwanaki kadan bayan da aka kama manyan jami'an FIFA a wani matakin binciken karbar hanci da rashawa da Amurka ke yi.

A watan Fabrairun badi ne za a sake zaben shugaban hukumar.

A can baya dai Mista Platuini ya yi biris da kiran da aka yi masa na son tsayawa takarada Mista Blatter.