Luiz na fatan Di Maria zai koma PSG

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luiz da Di Maria sun murza leda a Benfika ta Portugal

David Luiz na fatan Angel Di Maria zai koma Paris St-Germain, bayan da ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin fitattun 'yan wasan tamaula a duniya.

Di Maria wanda ya koma Manchester United a bara, bai halarci atisayen da United ta je a Amurka ba.

Tuni kuma kocin United Louis van Gaal ya ce bai san dalilin da Di Maria bai halarci atisayen ba, hasali ma bai san inda dan kwallon yake ba.

Kociyan PSG Laurent Blanc ne ya bayar da sanarwar cewar daf suke da kulla yarjejeniyar sayo Di Maria daga Manchester United.

Luiz dan kwallon Brazil ya ce duk kungiyar da Di Maria yake yi wa wasa sai ka ga ya kawo gagarumin cigaba.

Di Maria da Luiz sun taka leda a Benfica daga tsakanin 2007 da kuma 2010.