An wanke Mo Farah kan zargin kwayoyi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mo Farah zakaran tseren mita 5,000 da kuma 10,000

Hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-gujen Burtaniya ba ta samu Mo Farah da aikata ba dai-dai ba kan binciken zargin kocinsa Alberto Salazar da yin ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari.

Wani shirin BBC Panorama ne ya zargi Salazar da koyar da yadda ake lakantar yin ta'ammali da kwayoyin, zargin da ya ki amincewa da shi.

Babu wurin da aka samu Mo Farah da laifin yin amfani da kwayoyin masu kara kuzarin.

Salazar dan Amurka ya yi aiki da 'yan wasan tsalle-tsallen Burtaniya a matsayin jami'in tuntuba tun daga 2013.

Farah na shirin kare kambunsa a tseren mita 5,000 da kuma na 10,000 na duniya da Beijing za ta karbi bakunci.