Wenger ya doke Mourinho a karon farko

Image caption Sau 14 Wenger ya kara da Mourinho, a inda ya samu nasara a wasa daya suka yi canjaras a karawa 6

Arsenal ta lashe Community Shield na bana, bayan da ta doke Chelsea da ci daya mai ban haushi a fafatawar da suka yi a Wembley ranar Lahadi.

Alex Oxlade-Chamberlain ne ya ci wa Arsenal kwallo a minti na 24 da fara tamaula da hakan ya ba ta damar daukar Community Shield din.

Wannan shi ne karo na 21 da Arsenal ta buga Community Shield, yayin da ta dauka sau 13, ita kuwa Chelsea ta buga karo na 12, a inda ta dauka sau hudu.

Wannan kuma shi ne karon farko da Arsene Wenger ya samu nasara a kan Jose Mourinho, bayan da suka hadu a wasanni daban-daban sau 14, kuma suka buga canjaras a karawa 6.

Ana buga Community Shield ne tsakanin wanda ya lashe kofin Premier da kuma wanda ya dauki kofin FA bara, domin share fagen fara gasar Premier bana a ranar Asabar mai zuwa.