Na shirya amsa kiran Nigeria - Obafemi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obafemi Martins na fatan Sunday Oliseh zai gayyace shi tawagar Super Eagles

Tsohon dan kwallon tawagar Super Eagles, Obafemi Martins, mai taka leda a Seattle Sounders ya ce a shirye yake ya amsa kiran Nigeria.

Rabon da Nigeria ta gayyaci Martin tun a karawar da ta yi da Kenya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya, kuma sau daya a shekaru uku.

Duk da cewar dan wasan yana cin kwallaye a fafatawar da yake yi da kuma Ikechukwu Uche, ba'a ba shi goron gayyata cikin tawagar da ta wakilci Nigeria a kofin duniya da aka yi a Brazil ba.

Martin ya shaida wa BBC cewar "An samu sauyi a Nigeria, kuma idan sabon koci Sunday Oliseh ya gayyace ni, zan karbi damar da hannu biyu".

Dan kwallon wanda ya fara wasa da FC Ebedei a Nigeria ya buga tamaula a Italiya da Ingila da Rasha da Spaniya da kuma Amurka.

Tun kuma da ya koma Seattle da murza leda ya ci kwallaye 35 ya kumu taimaka aka zura 20 a raga daga wasanni 71 da ya yi a Amurkan.