Sudan ta Kudu za ta kara a wasan Olympics na 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da Sudan ta Kudu za ta fafata a wasan neman shiga babbar gasa ta Duniya

Sudan ta Kudu ta samu amincewa daga kwamitin shirya gasar wasan Olympics, na ta aike da tawagarta zuwa gasar wasan badi a birnin Rio de Janeiro.

Hakan kuma ya sa kasar ta zamo ta 206 a cikin mambobin hukumar da za su fafata a wasannin Olympic a duniya.

Shekaru hudu da suka gabata ne kasar Sudan ta Kudun ta samu 'yancin cin gashin kan ta, kan haka wuri ya kure mata na samun shiga gasar Olympics din na shekara ta 2012 da aka yi a birnin London.

Wani dan gasar wasan gudun fanfalaki dan kasar Sudan ta Kudun Guor Marial, da ya fafata a wadancan wasannin karkashin tutar Olympics, ya ce wasu yanzu karin 'yan Sudan ta Kudun zasu hadu da shi a wasan mai zuwa.

Sudan ta Kudu tana da tawagar kwallon kafa ta maza da za ta buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2018 a Rasha.