Crystal Palace ta sayi Connor Wickham

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan kwallon ya yi shekaru hudu a Sunderland da taka leda

Kungiyar Crystal Palace ta sayo Connor Wickham daga Sunderland kan kwantiragin shekaru biyar kan kudi £7m.

Wickham wanda ya sabunta zamansa a Sunderland tsahon shekaru hudu a Disamba, ya koma kulob din kan kudi £8m daga Ipswich a 2011.

Dan wasan mai shekaru 22, ya buga tamaula shekaru hudu a Sunderland, inda ya yi wasanni 91 ya kuma ci kwallaye 15.

Crystal Palace za ta iya kara kudin da za ta biya Wickham da zai kai £9m, idan ya taka rawar gani a kungiyar.

Palace ta dauki 'yan kwallo hudu kenan a bana da suka hada da mai tsaron raga Alex McCarthy da Yohan Cabaye da kuma Patrick Bamford da ta dauko aro daga Chelsea.