Enner Valencia zai yi jinyar makwonni 12

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enner Valencia ba zai fara buga wasan Premier bana ba

Dan kwallon West Ham United, Enner Valencia zai yi jinya ta makwonni 10 zuwa 12.

Valencia mai shekaru 25 ya ji rauni ne a kafarsa, bayan da ya ci kwallo a karawar da West Ham ta buga 2-2 da Astra Giurgiu a wasan neman gurbin shiga gasar Europa.

West Ham na fatan ba sai likitoci sun yi wa dan wasan tiyata ba, sai dai zai yi jinyar makwonni uku nan gaba, inda zai rika amfani da takalmi na musamman na kariya.

Valencia ya ci kwallaye hudu a wasanni 32 da ya buga wa West Ham gasar Premier bara.

West Ham ta ce za ta duba yiwuwar sayo wani dan wasan da zai maye gurbin Valencia, har ma ana rade-radin Raul Jimenez na Atletico Madrid za ta dauko.