Za a hana shan kwayoyi a Olympic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a hukunta wadanda suka lashe kyautar Olympic da magudi

Shugaban hukumar Olympic na duniya, Thomas Bach ya ce kwamitinsa zai dauki matakin ba-sani-ba-sabo idan ya tabbatar cewa mutanen da suka lashe lambobin yabo a gasar sun sha magungunan kara kuzari.

An yi zargin cewa akwai alamomin tambaya a kan gwajin jinin da aka yi wa mutane uku-uku a cikin dukkanin rukunin wadanda suka yi nasarar samun lambobin yabo a gasar da aka yi a shekarun 2001 da 2012.

Tsohuwar daraktar ladabtarwa a kan amfani da kwayoyin kuzari ta hukumar wasannin Ingila, Michele Verroken, ta ce akwai sarkakiya a kan yadda ake aiwatar da gwaje-gwajen jinin 'yan wasan.

Tana mai cewa akwai bukatar a sake gwajin jinin na su kafin a dauki matakin ladabtarwa a kansu: