Roma ta sayi Dzeko kan kudi £14m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dzeko ya bar City ne bisa sayo Sterling da aka yi daga Liverpool

Dan kwallon Manchester City, Edin Dzeko zai koma Roma ta Italiya da murza leda kan kudi £14m.

Dzeko mai shekaru 29 dan wasan tawagar Bosnia-Hercegovina ya koma City da taka leda ne a Janairun 2011 daga Wolfsburg kan kudi £27m.

Kuma a kakar bara ya sabunta zamansa a Ettihad zuwa shekaru hudu.

A baya daman kocin City, Manuel Pellegrini ya fada cewar Dzeko zai iya barin Ettihad, bisa sayo Raheem Sterling daga Liverpool kan kudi £49m da ya yi.

Dzeko shi ne kan gaba a matsayin dan wasan City da ya fi yawan cin kwallaye a inda ya zura 15 a raga a gasar Premier a kakar 2012-13.

Sai dai kuma kwallaye shida ya ci a wasanni 32 da ya buga wa Manchester City a bara.