Rafael zai koma Lyon da murza leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shekaru bakwai Rafael ya yi a Manchester United

Dan wasan Manchester United Rafael da Silva zai koma Lyon ta Faransa da taka leda kan kwantiragin shekaru hudu.

Rafael mai shekaru 25, wanda ya yi wa tawagar Brazil wasanni biyu, ya koma United ne tare da dan uwansa Fabio daga Fluminense a 2008.

Sai dai kuma tun lokacin da Louis van Gaal ya karbi aikin horas da United sau shida ya saka Rafael a wasa.

United ba ta je da Rafael atisayen da ta yi a Amurka ba, kuma tuni ta sayo Matteo Darmian daga Torino domin maye gurbin dan wasan.

Dan wasan ya lashe kofin Premier uku da na zakarun kungiyoyin duniya da League Cup a shekaru bakwai da ya yi a United.

Tun a Janairun 2014 dan uwan Rafael Fabio ya bar United ya kuma koma Cardiff City da murza leda.