Di Maria na murna zai koma PSG taka leda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekara daya Angel Di Maria ya yi wasa a Old Trafford

Angel Di Maria ya ce yana farin ciki da zai koma taka leda St-Germain daga Manchester United bayan shekara daya da ya yi a Old Trafford.

A bara ne United ta sayo Di Maria daga Real Madrid a matasayin dan wasan da aka sayo mafi tsada a Premier kan kudi £59.7m.

A ranar Talata likitocin PSG suka duba lafiyar dan wasan a shirin da yake yi komawa murza leda Faransa kan kudi £44.3m.

Di Maria ya shaidawa beIN Sports "Ina murna da zan koma Paris St-Germain, saboda kulob ne mai mahimmanci".

Dan wasan tawagar Argentina ya ci kwallaye hudu a fafatawa 32 da ya yi a United tun komawarsa Old Trafford a Agustan bara.