Enyimba ta bayar da tazarar maki 2 a Premier

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin Premier Nigeria mako na 21

Enyimba United ta buga 2-2 da Akwa United a gasar Premier wasannin mako na 21 da suka yi ranar Laraba.

Hakan ya sa Enyimba tana mataki na daya da maki 38 a teburin Premier, yayin Warri Wolves ke matsayi na biyu da maki 36, Sunshine ma tana da maki 36 sai dai kuma wasanni 20 ta yi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Nasarawa United ta doke El-Kanemi Warriors da ci 4-2, a inda Kano Pillars ta doke Heartland da ci 2-1.

Rangers kuwa daya mai ban haushi ta doke FC Taraba, yayin da Kwara United ta samu nasara a kan Dolphins da ci 2-1.

Ga sakamakon wasannin mako na 20 da aka yi:

  • Nasarawa Utd 4-2 El-Kanemi
  • Lobi Stars 3-0 Bayelsa Utd
  • Akwa Utd 2-2 Enyimba
  • Rangers 1-0 FC Taraba
  • Warri Wolves 3-0 FC Ifeanyiubah
  • Abia Warriors 2-0 Giwa FC
  • Kwara Utd 2-1 Dolphins
  • Shooting Stars 2-1 Wikki Tourists
  • Kano Pillars 2-1 Heartland