Murray ya sha kashi a hannun Gabashvili

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Andy Murrayya ce ya ji kayen da aka yi masa kamar a mafarki.

Dan wasan tennis na uku a duniya dan Biritaniya Andy Murray ya sha kayen ban-mamaki a zagaye na biyu na gasar tennis ta Washington, a hannun dan kasar Rasha Teymuraz.

Gabashvili bai yi wani fice a wasan tennis ba.

Murray, mai shekaru 28, ya zabi shiga wata gasa kafin gasar tennis ta Amurka, US Open, wadda za a fara ranar 31 ga watan agusta a birnin New York.

Andy Murraya ya sha kaye ne da ci 6-4 4-6 7-6 a hannun dan kasar rashana mai shekaru 30, wanda kuma shi ne 53 a jeren gwanayen tennis na duniya.

Murrya ya bayyana rashin nasarar da cewa kamar a mafarki.