Di Maria ya koma Paris St-Germain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Angel Di Maria ya ce ya kagu ya soma sanya rigar PSG.

Dan wasan Manchester United Angel Di Maria ya koma Paris St-Germain bayan kulob din ya saye shi a kan £44.3m.

Dan wasan, mai shekaru 27, ya bar United ne bayan kulob din ya sayo shi daga Real Madrid a kan £59.7m a bara.

Di Maria ya sanya hannu a kan kwantaragin shekaru hudu da kulob din na PSG bayan an gudanar da bincike kan ingancin lafiyarsa a kasar Qatar ranar Talata.

Dan wasan ya ce,"Ina alfahari matuka, kuma na kagu na fara sanya rigar Paris St-Germain."