Pallegrini ya tsawaita kwantigiri da Man City

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Pellegrini ya tsawaita kwantiragi da Man City

Kociyan Manchester City Manuel Pellegrini, ya sake sanya hannu a kan tsawaita kwantiraginsa da kulob din har zuwa shekarar 2017.

A badi ne dai kwantiragin Mista Pellegerini zai kare, amma yanzu zai ci gaba da kasancewa kociyan kulob din har zuwa kakar wasanni biyu nan gaba.

Mista Pellegrini ya ce "Ina alfaharin kasancewa shugaban Manchester City, ina da kwararrun 'yan wasa da suke fitar da kulob din kunya a ko yaushe."

Kulob din ya kuma sabunta kwantiragin mataimakan Mista Pellegrini guda uku da suka hada da Ruben Cousillas da Xabier Mancisidor da kuma Jose Cabello.

Wannan al'amari dai ya kawar da hasashen da ake cewa kociyan Bayern Munich Pep Guardiola ne zai maye gurbin Pellegrini a Man City.