Pellegrini ya sabunta kwantagarinsa a City

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan City suna jinjinawa Pellegrini

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya sabunta kwantaraginsa domin ci gaba da jagorantar kungiyar har zuwa shekara 2017.

Dan kasar Chile din a watan Yunin 2013 ya maye gurbin Roberto Mancini a matsayin kocin City.

"Ina alfahari da kasancewa kocin Manchester City," in ji Pellegrini.

Kafin sabunta kwantaragin, yarjejeniyarsa za ta kare ne a karshen kakar wasa mai zuwa.

A baya ana jita-jitar cewar za a kori Pellegrini domin kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya maye gurbinsa.