Uefa: United za ta hadu da FC Brugge

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Manchester ba ta buga gasar zakarun Turai ba a bara

Manchester United za ta hadu da Club Brugge ta kasar Belgium a wasan kifa daya kwala a gasar zakarun Turai.

Kungiyar Celtic ta Scotland kuwa za ta hadu ne da Malmo ta Sweden.

Za a buga wasa gida da waje kafin an samu kungiyar da za ta kai wasan zagayen farko na gasar.

Za a yi bugun farko a ranakun 18-19 ga watan Agusta da kuma 25-25 ga watan Agusta.

Sauran wasannin:

  • Celtic V Malmö
  • FC Astana V Apoel Nic
  • FC Basel V Maccabi Tel Aviv
  • Lazio V Bayer Levkn
  • Man Utd V Club Brugge
  • SK Rapid Vienna V Shakt Donsk
  • Skenderbeu Korce V Dinamo Zagreb
  • Sporting V CSKA
  • Valencia V Monaco