Neymar zai yi jinyar makwonni biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar ya buga wa Brazil gasar Copa Ameria da aka yi a Chile a bana

Neymar ba zai buga wa Barcelona wasannin farko da za ta yi a bana ba, sakamakon jinya da zai yi.

Dan wasan dan kwallon Brazil na fama da kumburin mukamuki, yayin da likitocin kulob din ke duba lafiyarsa.

Neymar zai yi jinyar makwonni biyu, wanda hakan na nufin ba zai buga wasan European Super Cup da Sevilla ranar Talata ba da Spanish Super Cup da Athletic Bilbao ranar 14 da kuma 17 ga watan Agusta.

Haka kuma dan kwallon ba zai buga wasan da Barcelona za ta yi da Athletic Bilbao a gasar La Liga ranar 23 ga watan Agusta ba.

Neymar mai shekaru 23, ya ci kwallaye 39 a raga, wanda ya taimakawa Barcelona lashe kofuna uku a bara.