Stoke za ta iya sayo Xherdan Shaqiri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool ce ta doke Stoke City har gida a gasar Premier ranar Lahadi

Kocin Stoke City, Mark Hughes ya ce za su iya sayo dan kwallon Inter Milan, Xherdan Shaqiri duk da cewa tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu ta gamu da cikas.

Stoke ta amince ta sayo Shagiri kan kudi £12m, daga baya ta janye daga cinikin a watan Yuni bayan da dan kwallon ya ki cewa komai kan tayin da aka yi masa.

Shagiri mai shekaru 23, ya halarci filin wasan Stoke wato Britannia Stadium a karawar da Liverpool ta samu nasara da ci 1-0 a gasar Premier da suka yi ranar Lahadi.

Hughes ya kara da cewa yana fatan za su kara yunkurin sayo dan wasan duk da cewar sun ci karo da tsaiko a baya.