Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Kurarin Kwarkwada da Jirgi Bahago babu kisa a wannan damben

An fafata a wasannin damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria da sanyin Lahadi.

An fara da karawa tsakanin Shagon Hafsat na Kaduna daga Kudu da Bahagon Abba daga Arewa, kuma a turmin farko Bahagon Abba ya yi kisa.

Fafatawa tsakanin Shagon Jafaru daga Kudu da Shagon Bunza daga Arewa turmi biyu suka yi babu kisa Sarkin gida na Jafaru Kura ya raba karawar.

Haka ma gumurzu tsakanin Shagon Shagon Alhazai daga Arewa da Matawallen Kwarkwada ta kayatar kuma turmi uku suka yi babu wanda ya yi nasara.

Shi ma dambe tsakanin Sojan Dogon Jango daga Arewa da Bahagon mai Maciji an biya 'yan kallo, kuma turmi biyu suka yi babu kisa a karawar.

Wasan Kuran Kwarkwada daga Kudu da Jirgi Bahago daga Arewa bai wani kayatar ba, kuma turmi biyu suka yi Sarkin Gida ya ce su bari haka.

Damben da aka yi tsakanin Garkuwan Mai Caji daga Kudu da Bahagon Alin Tarara sun yi gumurzu matuka, sai dai turmi biyu kawai suka taka babu kisa aka raba su.