Trabzonspor ta dauki Dame N'Doye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dame ya taka rawa a Hull City a kakar wasan bara

Kungiyar Trabzonspor ta Turkiya ta dauki dan kwallon Hull City Dame N'Doye kan kudi £2.2m.

N'Doye mai shekaru 30, ya amince da yarjejeniyar shekaru uku da kungiyar dake buga gasar Turkiyar.

Dan wasan dan kwallon Senegal ya koma Hull City ne daga Lokomotiv Moscow ta Rasha, yayin da ya ci kwallaye hudu a gasar Premier bara.

Hull City ta rubuta a shafinta na twitter cewar tana yi wa Dame fatan alheri da kuma gode masa kan gudunmawar da ya bata.