West Brom ta sayo dan wasa mafi tsada a tarihi

Image caption Brown Ideye shi ne dan wasa da West Brom ta saya mafi tsada a bana

West Brom ta kulla yarjejeniya daukar Solomon Rondon kan kudi £12m a matsayin dan kwallon da ta saya mafi tsada a tarihi.

Dan kwallon da kungiyar ta sayo mafi tsada tun kafa West Brom shi ne dan wasan Nigeria Brown Ideye kan kudi £10m a bara.

West Brom din ta sayo Randon mai shekaru 25, dan kwallon Venezuela daga kungiyar Zenit St Petersburg ta Rasha.

Dan wasan ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu da West Brom din.

Randon shi ne dan kwallo na biyar da West Brom ta dauka a bana, bayan James McClean da James Chester da Rickie Lambert da kuma Serge Gnabry.