Barcelona ta lashe Uefa Super Cup na 5

Image caption Wannan ne karo na biyar da Barca ta dauki Uefa Super Cup

Barcelona ta dauki Uefa Super Cup na bana kuma na biyar jumulla, bayan da ta sha da kyar a hannun Sevilla da ci 5-4 a wasan da suka kara ranar Talata.

Sevilla wacce ta lashe Europa League ce ta fara zura wa Barcelona mai rike da kofin zakarun Turai kwallo ta hannun Ever Banega daga bugun tazara.

Lionel Messi ne ya farke wa Barca kwallon da aka zura mata sannan ya kara ta biyu duk da bugun tazara, daga baya Rafinha da Luis Suarez kowannensu ya ci kwallo.

Sevilla ta farke kwallayenta ta hannun Jose Antonio Reyes da Kevin Gameiro wanda ya ci daga bugun fenariti sai Yevhen Konoplyanka da ya ci ta hudu da hakan ya kai karawar da karin lokaci.

Dan wasan da Manchester United ke zawarci Pedro shi ne ya ci wa Barcelona kwallo ta biyar da ta zama raba gardama.

Rabon da Barcelona ta dauki kofin tun 2011, kuma hakan ya sa ta yi kan-kan-kan da AC Milan a yawan lashe Uefa Super Cup sau biyar kowannensu.