An gargadi Pedro ka da ya koma United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United na son sayo Pedro domin ya maye gurbin Di Maria

Tsohon dan kwallon Bulgaria, Hristo Stoichkov ya gargadi Pedro da kada ya koma Manchester United taka leda.

Stoichkov ya kwatanta Louis van Gaal a matsayin dandagajin kociya wanda yake lalata kungiyoyin da ya horas.

An ruwaito cewar United tana son sayo Pedro daga Barcelona, domin ya maye gurbin Angel Di Maria wanda ya koma Paris St-Germain kan kudi £44.3m.

Stoichkov mai shekaru 49, wanda ya taka leda karkashin jagorancin Van Gaal ya ce "Ban taba karbar umarni daga kocin ba, kuma da zarar Pedro ya je United kwallonsa za ta zube".

Van Gaal ya horas da Barcelona tsakanin 1997 zuwa 2000, yayin da ya lashe kofunan La Liga da Copa del Rey da kuma Uefa Super Cup.